Hukumar jin dadin Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta sanar da kammala jigilar dawo da alhazan Najeriya daga ƙasar Saudiyya, inda jirgin ƙarshe ɗauke da alhazan Jihar Zamfara zai sauka rana Talata 23 ga Yunin shekarar 2026.
Hukumar ta bayyana cewa kammala jigilar alhazan, ya kawo ƙarshen dukkan ayyukan Hajjin bana, wanda ya haɗa da kaiwa da kuma dawo da dubban alhazan Najeriya daga ƙasa mai tsarki.
Sai dai hukumar ta ce har yanzu akwai alhazai ‘yan Najeriya (12) da ke shan magani a asibitoci daban-daban na Saudiyya.
-
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta rufe shari’arta kan Nasir El-Rufa’i
-
Ministar Abuja ta nesanta kanta daga zargin naɗin mataimaka bakwai
NAHCON ta ce tana sa ido sosai kan halin da suke ciki tare da shirya yadda za a dawo da su gida Najeriya da zarar an sallame su daga asibiti.
Hukumar ta bayyana cewa shirye-shiryen aikin hajjin shekarar 2027 mai kamawa zasu kankama nan da kowane lokaci, domin ganin an cimma nasara fiye da yadda ta faru a wannan shekarar.
