Gwamnatin Burkina Faso ta sanar da haramta wa wasu fitattun malaman addinin Musulunci guda biyu, gudanar da wa’azi da sauran ayyukan da suka shafi koyar da addini a faɗin ƙasa.
Mahukuntan ƙasar sun bayyana cewa an ɗauki matakin ne bayan zargin cewa malaman sun yi kalamai masu tsauri da ke iya haddasa rikice-rikice tare da yin barazana ga zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankalin al’umma.
-
Amurka da Iran Sun Fitar da Saƙonni Masu Saɓani Yayin Da Ake Kokarin Cimma Yarjejeniya.
-
Tsofaffin manyan hafsoshin soja da ‘yan sanda sun bayyana ra’ayoyi mabambanta kan‘yan sandan jihohi
Gwamnatin ta ce matakin na daga cikin kokarinta na tabbatar da tsaro da kare zaman lafiyar kasa, musamman a wannan lokaci da Burkina Faso ke fuskantar ƙalubalen tsaro a wasu yankunanta.
Ya zuwa yanzu dai ba a ji martanin malaman da abin ya shafa kan wannan mataki da gwamnati ta ɗauka ba.