Hukumar yaƙi da cutar  ƙanjamau ta Majalisar Ɗinkin Duniya, UNAIDS, ta yi gargaɗin cewa dakatar da tallafin da Amurka ke bai wa Afirka ta Kudu na yaƙi da cutar HIV/AIDS na iya janyo asarar rayuka tare da kawo koma baya ga nasarorin da aka samu cikin shekaru masu  yawa.

Babbar Daraktar UNAIDS, Winnie Byanyima, ta bayyana haka gabanin wani taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan yaƙi da cutar HIV/AIDS. Ta roƙi gwamnatin Amurka da ta sake nazarin matakin, tana mai cewa cire tallafin ba zato ba tsammani na iya jefa rayuwar dubban mutane cikin haɗari.

A cewarta, shirin tallafin Amurka na PEPFAR ya kasance yana bayar da kusan dala miliyan 400 a duk shekara domin tallafa wa ayyukan yaƙi da cutar HIV/AIDS a Afirka ta Kudu.

Afirka ta Kudu ce ƙasar da ke da mafi yawan masu ɗauke da kwayar cutar HIV a duniya, inda sama da mutane miliyan takwas ke rayuwa da cutar. Tallafin na Amurka ya kasance yana ɗaukar nauyin ma’aikatan lafiya kusan dubu 15 tare da taimakawa wajen gudanar da shirye-shiryen kula da masu cutar.

Sai dai Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce matakin rage tallafin ya samo asali ne daga wasu saɓanin manufofi tsakanin ƙasashen biyu, tana mai cewa Afirka ta Kudu na da ƙarfin da za ta iya ɗaukar nauyin shirye-shiryen lafiyarta.

UNAIDS ta kuma yi gargaɗin cewa rage tallafin ƙasashen duniya ga shirye-shiryen yaƙi da HIV na iya haifar da ƙarin kamuwa da cutar tare da kawo cikas ga burin kawo ƙarshen annobar AIDS nan da shekarar 2030.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *