Majalisar Dattawan Amurka, wadda Jam’iyyar Republican ke da rinjaye a cikinta, ta amince da wani ƙuduri da ke buƙatar Shugaban Ƙasa, Donald Trump, ya dakatar da yaƙin da ake yi da Iran ko kuma ya nemi amincewar Majalisar Dokoki kafin ya ci gaba da duk wani matakin soja.

A ƙuri’ar da aka kaɗa ranar Talata, wasu ’yan Republican sun haɗa kai da ’yan Democrat, inda suka amince da ƙudurin da ƙuri’u 50 kan 48.

Tun da farko, Majalisar Wakilan Amurka ta amince da irin wannan ƙuduri a farkon watan nan.

Ƙudurin ya zo ne a lokacin da wasu ’yan Republican a Majalisa ke nuna shakku kan shirin zaman lafiya da Trump ya cimma da Iran, yayin da yaƙin da ba ya samun karɓuwa a wajen jama’a ke gab da shiga wata na biyar.

Trump ya soki ƙudurin a daren Talata, yana mai cewa “An kawo shi a lokacin da bai dace ba kuma ba shi da wani tasiri.”

Sai dai wannan ƙuduri alama ce kawai ta matsayar majalisa, domin ko da ya samu amincewar dukkan majalisun dokoki, ba za a aika wa Trump domin ya sanya hannu a kai ba, kuma ba shi da ƙarfin doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *