Cibiyar kula da matsalar yoyon fitsari ta Ƙasa da ke Ningi a Jihar Bauchi ta sanar da fara shirin tiyata da magani kyauta ga marasa lafiya daga ko’ina cikin Najeriya.
A cewar sanarwar da cibiyar ta fitar, za a gudanar da shirin daga ranar 6 zuwa 10 ga watan Yulin 2026 tare da goyon bayan Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIA) da gidauniyar Fistula Foundation ta Amurka.
Sanarwar ta kara da cewa duk ayyukan da suka haɗa da rajista, duba marasa lafiya, gwaje-gwajen dakin bincike, tiyata, magunguna, kwanciya a asibiti da ciyar da marasa lafiya za su kasance kyauta.
- Mun rabawa dubban Almajirai Naman Sallah a bana -Hukumar kula da Almajirai
-
Sokoto a ƙarfafa yaƙi da mace-macen mata da yara hanyar wayar da kan al’umma
Haka kuma, cibiyar za ta tallafa wa marasa lafiya da kuɗin sufuri bayan sallamarsu daga asibiti, tare da samar musu da rijistar lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN) da sauran ayyukan tallafin walwala.
Cibiyar ta buƙaci marasa lafiya su fara zuwa cibiyar daga ranar 4 ga watan Yuli domin gudanar da rajista da sauran shirye-shiryen karɓarsu.
Har ila yau, cibiyar ta ce tana kan titin Kano a garin Ningi na Jihar Bauchi kuma tana karɓar marasa lafiya daga dukkan sassan Najeriya.
NOFIC Ningi cibiyar gwamnatin tarayya ce da aka kafa domin kula da mata masu fama da matsalar yoyon fitsari, tare da samar musu, magani da tiyata kyauta domin dawo da lafiyarsu da martabarsu.
