Ƙungiyar da za ta lashe gasar Firimiyar Najeriya (NPFL) ta 2026/2027 za ta samu sakamakon kyautar kuɗin da bai gaza naira biliyan 1 ba, wanda shi ne ladan kuɗi mafi girma a gasar ƙwallon ƙafa ta Najeriya.
Shugaban Hukumar Wasanni ta ƙasa, Shehu Dikko (NSC), shi ne ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa da manema labarai bayan wata babbar tattaunawa da Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya (NFF) ranar Talata a shelkwatar Hukumar Wasanni ta ƙasa da ke Abuja.
Dikko, wanda ya kuma bayyana wasu muhimman yanke shawara da aka ɗauka domin ƙarfafa ƙwallon ƙafa ta Najeriya, ya ce shugabannin NSC da NFF sun sake jaddada aniyar su ta bunƙasa ƙwallon ƙafa a Najeriya.
“Babban abin da aka fito da shi daga taron shi ne cewa zakaran gasar NPFL ta 2026/27 zai samu kyautar kuɗin da bai gaza naira biliyan 1 ba.
“Ƙungiyar da ta zo ta biyu za ta samu miliyan 500, yayin da ta uku za ta samu miliyan 300, bisa ga tabbatarwa daga hukumomin gasar,” in ji shi.
Dikko ya bayyana sabon tsarin ladan kuɗi a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin haɓaka darajar kasuwanci da ƙwarewa, a gasar cikin gida.
