Wasu mazauna yankin ƙaramar hukumar Alimoshon jihar Legas, na bayyana damuwa da yadda rashin kwashe shara akan lokaci ke shafar tasirin shirin tsaftar muhalli na wata-wata.
Al’ummar sun ce suna fitowa domin tsaftace muhallansu, kamfanonin kwashe shara ba sa zuwa kan lokaci, lamarin da ke sa ruwan sama da masu jari bola sake baza sharar.
- Mutum ɗaya ya jikkata yayin da wani abin fashewa ya tashi a Legas
- Kwalejin kimiyya da fasaha ta dakatar da Malamin da ya zane dalibai
Sai dai wasu mazauna yankin sun ce bai kamata a daina tsaftace muhalli ba saboda matsalar kwashe shara, duk da cewa tsafta nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa domin kare lafiya.
A cikin watan Afrilun shekarar 2026 ne gwamnatin Jihar Lagos ta dawo da shirin tsaftar muhalli na wata-wata, inda ake taƙaita zirga-zirga daga ƙarfe 6:30 na safe zuwa 8:30 na hantsi a ranakun Asabar na ƙarshe wata.