Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya zargi Gwamnatin Tarayya da shirya yadda za ta hana shi shiga takarar shugaban ƙasa ta shekarar 2027.
Da yake jawabi a wani shirin horas da shugabanci da ƙungiyar NextGen Mentorship and Leadership Initiative ta shirya a Jami’ar Madonna da ke Okija, Jihar Anambra, ranar Juma’a, Obi ya ce ana ƙoƙarin hana shi shiga zaɓe mai zuwa.
Ya ce:”Idan na faɗa muku abin da nake fuskanta a yau, da ba zan kasance a nan ba. Mutane sun tambaye ni, ‘Har yanzu za ka je Madonna?’ Sai na ce, ‘Eh, zan je.’ Suka ce, da duk abin da ke faruwa a Najeriya har yanzu za ka je? Sai na ce, ‘Eh. Na riga na ga mafi muni.’ A yau, Gwamnatin Tarayyar Najeriya na yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa ban zama ɗan takara a wannan zaɓe ba, amma ina tabbatar muku cewa ba za su yi nasara ba.”
Peter Obi ya a ƙara da cewa idan kana rayuwa ba tare da wata ƙalubale ba, to ba rayuwa kake yi ba. Kada ku mai da hankali kan ƙalubale, domin kullum za su kasance. Ni ba ƙalubalen nake kallo ba, burin da nake son cimmawa nake kallo. Ina mai da hankali ne kan amfanin da za a samu idan an kai ga burin, kuma wannan ne yake ƙarfafa ni.”
Obi ya kuma ƙalubalanci duk masu neman takarar shugaban ƙasa, ciki har da Shugaba Bola Tinubu, da su halarci muhawara ta bainar jama’a domin bayyana shirinsu ga Najeriya.
Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya shaida wa ɗaliban cewa ba son mulki ne ke motsa shi ba, illa burinsa na ganin Najeriya ta inganta.
- Shugaba Tinubu ya naɗa Abdulrazak Sa’ad Namdas a matsayin sabon Darakta Janar na Hukumar Raya Al’ummomin Kan Iyaka (Border Communities Development Agency – BCDA).
- Rundunar sojin ƙasar nan ta sauya fasalin aikin manyan jami’anta
- Jam’iyyar NDC ta yi Allah wadai da duk wani yunƙuri na amfani da bangaren shari’a domin taƙaita tasirin dimokuraɗiyya
Ya ce ba ya matsanancin son zama Shugaban Najeriya, abin da nake so shi ne ganin Nijeriya ta yi aiki. Ku je ku karɓi katin zaɓenku (PVC). Idan ba ku yi zaɓe ba, kuna lalata makomarku ne. Idan kun samu PVC, kada ku zaɓe ni saboda ni ɗan ƙabilar Igbo ne. Ba saboda ni ɗan Igbo ba ne nake neman takara, ku zaɓe ni ne saboda ni ne mafi cancanta.”Obi ya kuma yi tsokaci kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta soke wani hukunci na baya wanda ya umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi wa jam’iyyar NDC rajista.
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja ta soke hukuncin da ta yanke a baya wanda ya umurci INEC ta yi wa NDC rajista a matsayin jam’iyyar siyasa.
INEC ta yi wa NDC rajista a ranar 5 ga Fabrairu, 2026, bisa hukuncin da kotu ta yanke a ranar 10 ga Disamba, 2025.
Sai dai a ranar Juma’a, Mai Shari’a Isah Dashen ya bayyana cewa hukuncin farko ya saɓa wa kundin tsarin mulki domin an yanke shi ba tare da sauraron dukkan ɓangarorin da abin ya shafa ba.
Ya ce wannan kuskure ya sa dukkan matakan da aka ɗauka suka zama marasa inganci.
Kotun ta umarci dukkan ɓangarorin su koma matsayin da suke kafin hukuncin ranar 10 ga Disamba, 2025, sannan ta umurci masu ƙara su haɗa dukkan waɗanda abin ya shafa domin a warware rikicin yadda ya kamata.
Sai dai Obi ya ce wannan hukunci ba zai hana shi ƙalubalantar Tinubu da sauran ‘yan takara a zaɓen shekara mai zuwa ba.