Hukumar tsaro ta farin kaya  (DSS) ta saki wani mutum mai suna Nura Idris, bayan ta tsare shi bisa zargin alaƙa da ƙungiyar  Boko Haram.

Daraktan Hukumar ta (DSS) Oluwatosin Adeola Ajayi, ne ya bayar da umarnin a ranar Asabar, bayan rahoton kwamitin da aka kafa domin sake duba shari’ar da aka yi  masa, ya tabbatar da cewa babu wata hujja da ke alaƙanta shi da ƙungiyar.

Daraktan ya kuma umarci a baiwa matashin tallafin Naira miliyan Uku, domin taimaka masa farfaɗo da rayuwar da kasuwancin sa.

A wani bincike da hukumar tsaron ta gudanar, ta gano cewar matashin ɗan asalin ƙaramar hukumar Soba a jihar Kaduna, yana sana’ar noma da kiwo ne, gabanin kama shi a watan Yunin shekarar 2024.

A baya bayan nan dai hukumar tsaron ta kafa wasu kwamitoci dake sake nazari kan shari’o’i sama da 30, domin tabbatar da adalci ga waɗanda ta kama.

Kawo yanzu, rahotanni daga hukumar sun tabbatar da biyan diyyar fiye da Naira Miliyan 300, ga waɗanda ta kama kuma aka yankewa hukunci, akan laifukan da basu aikata ba.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *