Shelkwatar Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kogi ta fara bincike kan zargin kisan wata malamar makarantar firamare da aka ce an dake ta bayan ta ba ɗalibi horo a Karamar Hukumar Olamaboro ta jihar.
Hakan na cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta ’Yan Sandan Jihar, SP Oyiza Salisu Afusat, ta fitar ranar Lahadi.
Oyiza ta ce an bayar da rahoton lamarin kisan kai a ofishin ’Yan Sanda na yankin Olamaboro a ranar 25 ga Yuni, 2026.
A cewar sanarwar, binciken farko ya nuna cewa a ranar 18 ga Yunin 2026, wani mai suna Abdullahi Ishaka, tare da wasu mata biyu, an zarge su da kai farmaki wata Makaranta mai suna (Brains Minds Nursery and Primary School) dake Ugbamaka, inda suka doki wata malama, Maryam Usman, mai kimamin shelaru 30, saboda ta ba ɗalibi horo.
- Sojojin Sun Ƙwato Makamai a Kasuwar Doya ta Tor Donga
- NDLEA ta kama mutane 583 Kan safarar miyagun ƙwayoyi a Adamawa
“An samu munanan raunuka a jikin wadda aka kashe kuma an fara kula da ita a asibiti kafin a tura ta zuwa Asibitin Iko-Ojo, Okpo, domin ci gaba da samun kulawa.
Sai dai ta rasu a ranar 25 ga Yunin 2026,” in ji sanarwar.
Afusat ta ce bayan samun rahoton, jami’an ‘Yan Sanda sun ziyarci wurin da lamarin ya faru da kuma gidan su marigayiyar, inda suka karɓi bayanan da suka dace.
Ta ƙara da cewa yanzu haka ana shirin kai gawar marigayiyar zuwa Asibitin Gwamnati, dake Ankpa, domin a yi mata gwaji da kuma gano musabbabin mutuwarta.
Mai magana da yawun ’Yan Sandan ta bayyana cewa wadanda ake zargi da hannu kan kisan malamar sun gudu kafin jami’an su isa garesu, inda ta kara da cewa ana ƙoƙari don kama su.
A cewarta, “Bayan an kama su, za a mika lamarin zuwa Sashen binciken laifuka na rundunar domin faɗaɗa bincike.”