Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta ayyana Olusegun Ola Osinkolu mai shekara 61 a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.
A cewar sanarwar EFCC, ana neman Osinkolu ne bisa zargin haɗa baki wajen aikata laifi, da yin jabun takardu da kuma karɓar kuɗi ta hanyar yaudara.
- Gwamnatin Indiya ta dakatar da ƙaddamar da sabon tsarin Whatsapp
- Babbar Kotun Tarayya ta tabbatar da halaccin shugabancin Sanata David Mark a jam’iyyar AD
- Bankin Duniya ya amince da bai wa Najeriya sabon rancen dala biliyan 1.25
Hukumar ta bayyana cewa Osinkolu ɗan asalin jihar Ekiti ne, kuma adireshinsa na ƙarshe da aka sani shi ne lamba ta 3, Chucks Onyebuchi, Lekki Phase 1, Victoria Island, jihar Legas.
A baya bayan nan hukumar EFCC na ƙarfafa bincike kan masu aikata manyan laifuka a faɗinƙasar.