Wikki Tourists FC ta bayyana kociya Bala Abubakar Mohammed a matsayin sabon mai horar da Ƙungiyar gabannin fara gasar Kasa mai daraja Aji na biyu ta NNL, ta kakar bana ta 2026/27.

Wikki Tourists ta sanar da haka ne a shafinta na Facebook ranar Asabar, yayinda ta yi masa maraba da kuma fatan samun nasara inda zai jagoranci tawagar a kakar wasa ta 2026/27.

Kociya Bala yana da Lasisin shaidar horarwa ta CAF B kuma yana da ƙwarewa mai yawa a fannin horarwa.

A baya can, Kociya Bala ya horar da ƙungiyoyi irin su Lobi Stars F.C da Niger Tornadoes F.C da Katsina United da Doma United F.C da kuma Zangai International ta Bauchi.

Haka kuma ya taɓa zama mataimakin kociyan tawagar ‘yan ƙasa da shekaru 20 ta Najeriya da kuma tawagar ‘yan wasan Olympic ta Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *