A ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata ne Dr Ibrahim Sheme, Shugaba Hukumar Daraktoci na Blueprint Radio  ya miƙa ragamar aiki ga wacce za ta gaje shi, Misis Olajumoke Omotola Ojudu, a matsayin Shugaban  Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Jami’ar National Open University of Nigeria (NOUN), bayan ya shafe shekaru goma yana jagorantar sashen.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ya mfitar a karshen mako, inda ya bayyana cewa Misis Ojudu gogaggiyar ma’aikaciya ce a cikin jami’ar, wacce ta kasance tana aiki tare da shi a matsayin mataimakiyar sa.

Sanarwar ta nuna cewa Misis Olajumoke Omotola Ojudu . Saboda kusancin da muka yi wajen aiki tsawon shekaru tana da cikakkiyar fahimta game da yadda sashen ke gudanar da ayyukansa da kuma manufofinsa.

Sai dai Dr Sheme ya bayyana cikakken yaƙinin cewa za ta iya jagorantar sashen yadda ya kamata tare da ɗaga darajarsa zuwa mataki mafi girma.

A yayin taƙaitaccen bikin miƙa ragamar aiki da aka gudanar a tsohon ofishinsa, ya bayyana cikakken amincewasa da ƙwarewarta wajen jagoranci.

Har il;a yau, Dr Sheme ya kuma yi kira ga dukkan ma’aikatan sashen da su ba ta cikakken haɗin kai da goyon baya domin ta samu nasarar ciyar da Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a gaba tare da ba da gudunmawa ga ci gaban jami’ar baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *