Hukumar yanayi ta Najeriya, NiMet, ta yi gargaɗin yiwuwar samun ambaliya a jihohi 27 na Najeriya, tsakanin 1 zuwa 10 ga watan Yuli, sakamakon ci gaba da ruwan sama mai ƙarfi.
A cikin sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce jihohin da ke cikin haɗari sun haɗa da Lagos, Ogun, Oyo, Osun, Ekiti, Kogi, Kwara, Kaduna, Katsina, Kebbi, Sokoto, Zamfara, Nasarawa, Plateau, Taraba, Adamawa, Borno, Delta, Edo, Abia, Imo, Anambra, Enugu, Akwa Ibom, Cross River, Rivers da Bayelsa.
NiMet ta bayyana cewa yawan ruwan sama da aka samu a watan Yuni ya sanya ƙasa gyatsewa, lamarin da ke rage mata ikon shanye ƙarin ruwan sama, abin da ka iya haifar da ambaliya a lunguna, birane da yankunan dake gaba.
- Jami’ar jin ƙai ta raba rigunan tsaron ruwa ga masu ceton rayuka a Kogin Kaduna
-
Ambaliya: Ghana na asarar Dala Miliyan 200 duk shekara -GMet
Hukumar ta kuma yi gargaɗin cewa ambaliyar na iya haddasa cunkoson ababen hawa, rufe hanyoyi, katse wutar lantarki da hanyoyin sadarwa, tare da lalata gonaki, tituna, gadoji da sauran muhimman ababen more rayuwa.
Saboda haka, NiMet ta shawarci jama’a da su rika bibiyar hasashen yanayi tare da share magudanan ruwa, sannan su guji tafiya ko tuƙi a wuraren da ruwa ya mamaye.
Hukumar ta buƙaci hukumomin agaji kamar NEMA, SEMA da sauran hukumomi su daura damarar shirin ko-ta-kwana, domin rage illolin da ka iya biyo baya.
