Jonathan

Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya musanta wani rahoton kafafen yaɗa labarai da ke zargin cewa an ba shi tayin Naira biliyan 500 domin ya tsaya takarar shugaban ƙasa don rage wa ɗan takarar jam’iyyar National Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ƙuri’u a yankin Kudu maso Kudu

Mai ba Jonathan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Dr. Ikechukwu Eze, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, inda ya ce rahoton ƙarya ne gaba ɗaya kuma ba shi da tushe.

Eze ya buƙaci ‘yan Najeriya su yi watsi da abin da ya kira ƙagaggen rahoto, wanda ya danganta wa Jonathan wata magana da bai taɓa yi ba.

Sai dai ya amince cewa yayin da lokacin siyasa ke ƙaratowa, ana yawan samun yaɗuwar bayanan ƙarya da kuma jingina wa mutane kalaman da ba su faɗa ba.

Ya buƙaci ‘yan Najeriya su yi watsi da rahoton baki ɗaya, tare da tabbatar da sahihancin duk wani labari mai tayar da hankali kafin su yada shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *