Shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce yaƙin da ƙasarsa ke yi da Rasha ya shiga wani sabon mataki, inda ya bayyana cewa fafatawar yanzu ta fi karkata zuwa sararin samaniya fiye da yaƙin ƙasa.

Zelensky ya bayyana haka ne cikin wani rubutu daya wallafa a shafinsa na X.

A cewarsa, sojojin Ukraine sun dakatar da ci gaban Rasha wajen kai farmaki, duk da tsananin asarar rayuka, lamarin da ya sa yaƙin ya koma amfani da fasahar zamani da ƙarfin hare-haren sama.

Zelensky ya ce Ukraine na samun ci gaba a wannan fanni amma babbar matsalar da ƙasar ke fuskanta ita ce rashin ingantaccen tsarin kariya daga makamai masu linzami na ballistic.

Ya bayyana cewa Ukraine ba ta gaji irin wannan tsarin daga tsohuwar Tarayyar Soviet ba, domin yawancin kayan sun kasance a Moscow.

Ya kuma jaddada cewa rashin mallakar makaman nukiliya ya sanya Ukraine cikin ƙasashen da ke fuskantar barazanar hare-hare ba tare da kariya irin ta manyan ƙasashe ba.

Shugaban na Ukraine ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa basira da fasahar zamani za su kasance mabuɗin samun nasara a wannan yaƙi.

Ya ƙara da cewa idan ƙawayen Ukraine suka ci gaba da tallafa mata da kuɗi da kayan yaƙi, sannan sojojinta suka ci gaba da tsayawa tsayin daka a fagen fama, za su iya ci gaba da fafatawa a sararin samaniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *