Rundunar sojin Mali ta ce wasu ‘yan bindiga sun kai hare-hare a wurare biyar daban-daban a faɗin ƙasar, fiye da watanni biyu bayan wasu mahara sun kai hari kan babban birnin ƙasar da sauran yankuna.

A cewar rundunar hare-haren sun faru ne a ranar Asabar a yankuna da suka haɗa da wani gari a arewacin ƙasar inda dakarun gwamnati da sojojin Rasha ke da sansani, da kuma wani gari da ke kudancin babban birnin Bamako..

Sojojin Mali sun bayyana cewa hare-haren sun shafi garuruwan Aguelhok da Anefis da Gao da Sevare da kuma Kenieroba

Kamfanin dillancin labarai AFP ya ruwaito cewa an kai hari kan wani gidan yari da ke Kenieroba, mai tazarar kilomita 74 daga Bamako, yana mai ambaton mazauna yankin da jami’an tsaro.

Rahoton ya ce faɗan ya fara ne da misalin ƙarfe 5:00 na safiyar yau Asabar agogon ƙasar.

A gefe guda, wata ƙungiyar ’yan tawaye ƙarƙashin jagorancin kabilar Tuareg ta tabbatar da cewa mayaƙanta sun kai hari kan garin Anefis da ke yankin Kidal a arewa maso gabashin Mali.

Kakakin Ƙungiyar ‘Yantar da Azawad (Azawad Liberation Front – FLA), Mohamed Elmaouloud Ramadane, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa mayaƙan ƙungiyar ne suka kai harin.

Bayan hare-haren da aka kai a ranakun 25 da 26 ga Afrilu, gwamnatin Mali da dakarun Rasha sun tura ƙarin sojoji zuwa Anefis, bayan da mayaƙan FLA tare da wata ƙungiya mai alaƙa da Al-Qaeda suka ƙwace. ikon garin Kidal.

Mali ta daɗe tana fama da hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai masu alaƙa da Al-Qaeda da ISIS (ISIL), baya ga tawayen ’yan awaren arewacin ƙasar.

Shekaru da dama ke nan da ’yan awaren ke fafutukar kafa ƙasa mai cin gashin kanta a arewacin Mali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *