Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya yi kira da a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin mabiya addinai domin bunƙasa zaman lafiya da zaman tare cikin lumana a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.

Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar baƙuncin Sakataren Vatican mai kula da Hulɗa da Ƙasashe, Archbishop Paul Gallagher, a birnin Sokoto.

Ya yaba wa al’ummar Katolika kan ƙoƙarinsu na inganta tattaunawa tsakanin addinai da ƙarfafa haɗin kan ƙasa da kuma tallafa wa harkokin tsaro.

A yayin ganawar, shugabannin biyu sun yi Allah wadai da kalaman ƙiyayya da yaɗa labaran ƙarya da kuma tabarbarewar ɗabi’u, suna masu cewa waɗannan abubuwa na ƙara rarrabuwar kawuna tsakanin mabiya addinai.

Sun kuma yi alƙawarin ƙara haɗin gwiwa wajen bunƙasa mutunta jun daa ƙarfafa tsaro da kuma magance matsalar da ake fuskanta ta ƙaruwa wajen ƙin bin addini a tsakanin matasa.

Haka kuma, sun buƙaci shugabannin addinai su yi aiki tare domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *