Tsohon Gwamnan Jihar Borno kuma jigo a jam’iyyar (APC), Ali Modu Sheriff, ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, Peter Obi, ba zai samu goyon bayan masu kaɗa ƙuri’a daga Arewacin Najeriya ba a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Sheriff ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata hira da ya yi a tashar talabijin ta Channels Television, inda ya kuma kare yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke tafiyar da yaƙi da matsalolin tsaro a ƙasar.

Sheriff ya kuma yi iƙirarin cewa magoya bayan tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ba sa goyon bayan duk wata haɗakar siyasa da za ta haɗa Kwankwaso da Peter Obi.

Da yake mayar da martani kan sukar da Peter Obi ke yi wa Shugaba Bola Tinubu game da matsalar tsaro, Sheriff ya ce matsalar tsaro ta daɗe tana addabar Najeriya tun kafin gwamnatin Tinubu ta hau mulki, saboda haka ya kamata a yi wa shugaban ƙasa hukunci bisa matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin magance matsalar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *