Alaƙa tsakanin ƙasashen Afirka ta Kudu da Ghana tayi tsami a baya bayan nan, sakamakon kashe wani matashi a zanga-zangar kyamar baƙi

Hukumomi a kasar Ghana sun yi watsi da buƙatar karɓar Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, wanda aka tsara zai kawo ziyarar aiki a farkon watan Agustan shekarar 2026.

Majiyoyi daga Accra sun tabbatar da cewa, soke ziyarar ya biyo bayan wata zanga-zanga da bore da ƴan ƙasar suka shirya, domin adawa da ziyarar Shugaban na Afirka ta Kudu a ƙasar Ghana.

Hukumomin Ghana sun fito fili sun bayyana cewa kare rayuka, tsaro, da mutuncin ƴan ƙasar su da ke ƙasashen waje, abune da ba za su taɓa yin wasa da shi ba.

Taƙaddama tsakanin ƙasashen biyu na ƙara tsami a baya bayan nan, biyo bayan rahoton kisan gillar da aka yi wa wani ɗan ƙasar Ghana mai suna Bashiru Isak, ɗan shekara 40, a yankin Khayelitsha da ke Cape Town, kisan da mahukunta a Pretoria suka musanta.

A wata sanarwa da rundunar ƴan sandan ƙasar (SAPS) ta fitar, ta yi iƙirarin mutuwar Bashiru Isak bata da alaƙa da zanga-zangar ƙyamar baƙi, an harbe shi ne a wani fashi da makami da aka yi a wani shagon aski.

A halin da ake ciki, gwamnatin Ghana ta gargaɗi Pretoria cewa ba za ta amince da wata ziyarar wani shugaba a nan gaba ba, har sai idan gwamnatin Cyril Ramaphosa ta ɗauki kwararan matakai na zahiri wajen hukuntawa tare da magance kyamar baki a ƙasar ta.

Sai dai Afirka ta Kudu na zargi hukumomin Ghana da rura wutar dambarwa ta hanyar amfani da labaran ƙarya don ɓata mata suna a idon duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *