Majalisar Dattawan Najeriya ta bayyana cewa ba ta da wata ƙorafi a gabanta dangane da cece-kucen da suka dabaibaye wata hukuma da ake takaddama a kanta, wato PFIPC.
Mai magana da yawun Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, ya shaida wa manema labarai bayan zaman majalisar a Abuja cewa Majalisar ba za ta shiga cikin lamarin ba har sai an gabatar mata da ƙorafi a hukumance daga ɗaya daga cikin ɓangarorin da ke takaddama ko kuma daga wani ɗan Najeriya.
A makonnin baya dai an samu cece-kuce bayan Babban Ma’aikacin Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya musanta wanzuwar hukumar PFIPC tare da wanda ke ikirarin jagorantar ta.
Sai dai Adeniyi Adeyemi Mathew ya musanta hakan, yana mai cewa fadar shugaban ƙasa ta san da hukumar.
Har ila yau, ya yi zargin cewa Babban Ma’aikacin Fadar Shugaban Ƙasa ya karɓi naira miliyan ɗari huɗu domin ba shi wannan muƙami, sannan ya nemi kashi 48 cikin ɗari na naira biliyan ɗaya da miliyan ɗari uku da aka ware wa hukumar a kasafin kuɗin shekarar 2026.
Da yake bayyana matsayar Majalisar Dattawa, Sanata Adaramodu ya ce lamarin ya shafi ɓangaren zartarwa ne, don haka su ne ya kamata su warware shi.
Ya kuma ƙara da cewa tunda batun yana gaban kotu, Majalisar ba za ta tsoma baki ba.
Ya kuma bayyana cewa duk da kasancewar an ware kuɗi ga hukumar a kasafin kuɗin shekarar 2026, Majalisar Dokoki ba ita ce ke ƙirƙirar ko saka sunayen hukumomi cikin kasafin ba, kuma ba aikinta ba ne tantance mutanen da aka naɗa shugabancin hukumomin gwamnati.
Sai dai ya ce idan aka shigar da ƙorafi a hukumance ga Majalisar Dattawa daga kowane ɓangare ko wani ɗan ƙasa kan sahihancin hukumar ko shugabanta, majalisar za ta binciki batun ta hanyar da doka ta tanada.