Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) ta sanar da ceto mutane huɗu da aka yi garkuwa da su a wani hari da masu garkuwa da mutane suka kai a yankin Yellow House da ke Mpape a Abuja.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar, ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:40 na dare ranar Laraba, 8 ga Yuli, 2026, lokacin da ake zargin masu garkuwa da mutane suka mamaye yankin tare da yin awon gaba da mazauna huɗu
- Gwamnatin Zamfara ta amince da hutun haihuwa na watanni 6 ga mata ma’aikata
- Tinubu ya ƙaddamar da ƙofar shiga birnin Abuja, ya ce alama ce ta haɗin kan ƙasa
- Sojoji sun kama wata da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi ga ‘Yan Ta’adda a Tafkin Chadi
Sanarwar ta ce bayan samun rahoton, Kwamishinan ‘Yan Sandan FCT, CP Ahmed Muhammed Sanusi, ya tura jami’an Sashen Yaƙi da Garkuwa da Mutane, da jami’an ofisoshin ‘yan sanda na Katampe da Mpape, tare da dakarun rundunar 24 Police Mobile Force Squadron domin kai ɗauki
Binciken farko ya nuna cewa maharan sun harbi mutane biyu kafin su tsere daga wurin.
Haka kuma, sun tilasta wa wasu mutane huɗu da suka yi garkuwa da su yin tafiya ta tsaunukan Jikoko zuwa dajin Ushafa.