Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da Ƙofar Shiga Birnin Abuja da akayiwa kwaskwarima, inda ya bayyana ta a matsayin alamar haɗin kan Najeriya, bambancin al’adu da kuma muradun da ‘yan ƙasa suka haɗa kai a kai
Haka kuma, ya yabawa Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, kan irin sauye-sauyen da yake kawowa Abuja ta hanyar aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa.
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ce ta wakilci shugaban ƙasar wajen bikin ƙaddamar da aikin a ranar Alhamis. Ta ce sabon fasalin ƙofar zai ƙara wa Abuja kima a matsayin cibiyar diflomasiyya da gudanarwar Najeriya, tare da kasancewa wata alama ta alfaharin ƙasa.
- Majalisar dattawa ta karanta wasikar da Shugaba Tinubu ya aike mata
- Ruwan sama ya lalata gidaje 20 da gonaki a Jihar Plateau
- Rashin Tsaro: Tinubu ya gana da jagororin hukumomin tsaro a Aso Rock
A cewarta, ƙofar ta ƙunshi maɓuɓɓugar ruwa da ke wakiltar jihohi 36 na Najeriya da Babban Birnin Tarayya (FCT), a wani yanayi na yiwa baƙi maraba da ta dace yayin da suke shiga babban birnin ƙasar.
An ƙaddamar da sabon Abuja City Gate, wanda ke ɗauke da wata maɓuɓɓugar ruwa da ke wakiltar jihohi 36 na Najeriya da Babban Birnin Tarayya, a matsayin wani ɓangare na bukukuwan cika shekaru uku da gwamnatin Tinubu ta yi da kuma bikin cika shekaru 50 da kafa Babban Birnin Tarayya.