Wata guguwar ruwa mai ƙarfi ta lalata gidaje sama da 20 da gonaki a al’ummar Nghassi da ke Mazaɓar Mandar, a Ƙaramar Hukumar Bokkos ta Jihar Plateau, lamarin da ya bar mazauna yankin ba tare da muhalli ba, kuma suna buƙatar agajin gaggawa na ɗan adam.

Guguwar ta tafka ɓarna a faɗin al’ummar yankir, inda ta ɗaye rukunonin gidaje, ta tumfuke bishiyoyi, ta rushe gine-gine, sannan ta lalata kaddarori na miliyoyin naira.

Wani mazaunin yankin, Mista Bulus Ayuba Ritji, ya bayyana cewa mamakon ruwan ya zo ne da iska mai ƙarfi wacce ta bar baya da ƙura ta ɓarna, lamarin da ya tilasta wa iyalai da dama neman mafakar ɗan lokaci a gidan maƙwabta da dangi.

A cewar Ritji, ko da yake babu rai da aka rasa, mutane da dama da abin ya shafa sun rasa gidajensu da kayan abinci, tufafi da sauran kayayyaki masu daraja, wanda hakan ya jefa su cikin damuwa da ƙunci.

Ya ƙara da cewa guguwar ta kuma lalata gonaki da sauran hanyoyin dogaro da kai na mazauna yankin, lamarin da ya ƙara ta’azzara halin da suke ciki.

Shugaban Matasa na Ƙaramar Hukumar Bokkos, Christopher Luka, ya yi kira ga ƙungiyoyin agaji da sauran ƴan Najeriya masu kishin ƙasa da su tallafa wa mutanen da abin ya shafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *