Kocin Moroco, Mohamed Ouahbi

Kocin Moroko Mohamed Ouahbi ya yi alkawarin cewa tawagarsa za ta dawo da ƙarfi bayan ficewarsu daga wasan kwata fainal na Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026 da Faransa ranar Alhamis, inda aka tashi wasa ci 2-0.

A cewarsa, za su ci gaba da ginawa yayin da suke Shirin zama cikin waɗanda za suyi haɗin gwiwa don daukar nauyin gasar mai zuwa ta 2030.

Ko a shekaru huɗu da suka gabata a kasar Qatar, Faransa ce ta cire moroko da ci 2-0 a matakin wasan kusa da karshe na Gasar Cin kofin duniya ta 2022.

Moroko ta yi fatan zarce ƙoƙarin da ta yi a Qatar, toh amma hakkarta bai cimma ruwa, yayinda Kyalian Mbappe ya zura kwallo daya tare da kuma baiwa Ousmane Dembele taimakon zura ƙwallo guda.

“Tawagar Faransa na da ƙarfi sosai. Mun fafata ne da ƙasar da ta shiga wasan ƙarshe na Gasar Cin Kofin Duniya sau 2 na ƙarshe, kuma ba su taɓa samun hazaka kamar yadda suke da ita yanzu ba,” in ji Ouahbi.

“Mun san za mu iya fafatawa, kuma abin da muke so mu yi shi ne mu yi aiki tukuru don mu yi fiye da haka a gaba.”

“Muna son mu yi nesan zango a gasar har ma da lashe Gasar Cin Kofin Duniya, don haka muna cikin baƙin ciki saboda mun sha kashi, amma dole ne mu yarda da hakan.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *