Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da kwamitin mutum 17 da zai tsara sabon kundin manufofin yaƙin neman zaɓensa na shekarar 2027.

A cewar wata sanarwa da Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Juma’a, an ɗora wa kwamitin alhakin nazarin yadda aka aiwatar da kundin manufofin zaɓen shekarar 2023 mai taken “My Commitment for Kano”, tare da tsara sabon kundi mai suna “Blueprint 2.0”.

Sanarwar ta bayyana cewa sabon kundin zai zama jagora ga manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Abba Kabir Yusuf idan aka sake zaɓensa a wa’adi na biyu tsakanin shekarar 2027 zuwa 2031.

An naɗa Dr. Aminu Magashi Garba a matsayin shugaban kwamitin, yayin da Dr. Yusuf Ya’u Gambo, Shugaban Hukumar Strategic Governance and Policy Coordination, zai kasance sakataren kwamitin.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da jami’an gwamnati da ƙwararru daga fannoni daban-daban, ciki har da lafiya da ilimi da noma da fasahar sadarwa da bincike da tsara manufofi.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya koma jam’iyyar APC ne a ranar 26 ga Janairu, 2026, bayan ficewarsa daga jamiyyar NNPP, wadda ya ci zaɓen gwamna a ƙarƙashinta a 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *