Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) sun ƙara ƙarfafa haɗin gwiwarsu domin inganta shirin tunkarar iftala’i da bayar da agajin gaggawa, musamman dangane da barazanar ambaliyar ruwa a sassan ƙasar.

Shugaban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu ne, ya bayyana hakan yayin da ya karɓi bakuncin Babbar Daraktar hukumar NEMA, Hajiya Zubaida Abubakar Umar, a hedikwatar rundunar dake Abuja.

Ya ce rundunar sojin ta kafa ƙungiyoyin bayar da agajin gaggawa a dukkan shiyyoyin shida na ƙasar domin gaggauta kai ɗauki ga yankunan da ke fuskantar haɗarin ambaliya da sauran iftala’i.

Haka kuma ya umurci Babban Jami’in Horaswa na rundunar da ya bai wa hukumar NEMA damar amfani da cibiyar horas da jami’anta domin gudanar da atisayen haɗin gwiwa da shirye-shiryen tunkarar bala’o’i.

Shaibu ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da na agajin gaggawa, inda ya bayyana cewa hakan ne zai taimaka wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

 

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *