Lamine Yamal ya ce Faransa ta fi cancanta ta ji tsoro da fargaba kafin babban fafatawar su ta kusa da na ƙarshe a Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026 akan ƙasar Spaniya.
La Roja ta samu tikitin zuwa matakin kusa da na ƙarshe bayan ta doke Belgium da ci 2-1 a Los Angeles, inda Mikel Merino ya shigo daga benci ya ci ƙwallon da ta tabbatar da nasarar.
Spaniya ta kai wasan kusa da na ƙarshe na Gasar Cin Kofin Duniya a karo na biyu kenan kawai tun bayan 2010, lokacin da suka ci gasar a Afirka ta Kudu.
- Tennis: Zverev ya kawo karshen burin Fery na buga wasan ƙarshe na Wimbledon 2026
- City ta sayi mai tsaron raga Charles
- Kocin Morokoya yi alkawarin cewa tawagar za ta dawo da ƙarfi bayan ficewa daga Gasar Cin Kofin Duniya
Yanzu Spaniya za ta fafata da Faransa domin neman gurbi a wasan ƙarshe, kuma Yamal ya ce babu dalilin da ya sa zakarun na Turai za su ji tsoron haduwar.
“Idan akwai wanda ya kamata ya ji tsoro, shi ne su. Mun cire su a Gasar Euro 2024 da kuma Nations League ta 2024-25],” in ji Yamal.
“Mun kasance ƙasashe biyu masu ƙarfi, a tunani na kuma waɗanda suka fi kyau, amma ba mu da tsoro.”
Shima kocin Spaniya, Luis de la Fuente, wanda yanzu ya jagoranci wasanni da yawa a Gasar Cin Kofin Duniya da Euro ba tare da ya sha kaye ba fiye da kowane koci (Wasanni 13, Nasara12, Canjaras1), ra’ayinsa ya zo ɗaya da Yamal.
“Abu ne na adalci idan muka ce za mu yi aiki don mu doke su; ina ganin su ma suna jin fargabar haɗuwar,” in ji De La Fuente game da Faransa.
“Mune kadai ƙasar da ta doke su wasanni biyu a jere. Babbar tawaga za ta fafata da wata babbar tawaga.”