Declan Rice, Marc Guehi da Reece James sun ƙara ƙarfafa tawagar Ingila yayin da su ka dawo daga jinyar raunin da suka samu gabannin fafata wasan kwata-final na Gasar Cin Kofin Duniya da Norway.

Rice ya yi fama da rashin lafiya tun bayan nasarar da suka samu a zagaye na 16 a Mexico, yayin da Guehi ya kasa halartar artisayen Ingila a Kansas City ranar Alhamis saboda raunin da ya samu a ƙafarsa.

Sai dai duka ‘yan wasan biyu sun halarci atisayen tawagar a Miami ranar Juma’a, kafin fafatawar ranar Asabar da Norway a wannan birni.

James ma ya shiga atisayen, wanda shi ne na farko gare shi tun bayan raunin da ya samu a ƙafa a wasan rukuni na biyu na Ingila da Ghana.

Kocin Ingila, Thomas Tuchel ya bayyana cewa duka ‘yan wasa ukun za a iya zaɓar su ranar Asabar domin karawa da Norway.

“Mun samu halartar kowa da kowa yayin atisayen. Wannan shi ne mafi kyawun labari,” in ji Tuchel a taron manema labarai na kafin wasa.

“Sai wanda muka yi niyyar zaɓa in banda dan wasan da aka dakatar [Jarell Quansah].”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *