Tawagar Golden Eaglets ta Najeriya ta kammala Gasar ƙasar China na matasa ta 2026 da kunnen doki (1-1) da masu masauƙin baƙi China, bayan sun sha kaye sau biyu a jere.
Tawagar Najeriya ta ‘yan kasa da shekaru 17 Eaglets ta shiga wannan wasa ne bayan ta sha kaye a hannun Tanzania da Australia, amma ta buga wasa mai kyau a wasanta na ƙarshe.
Idor samuel ne ya fara ci wa Najeriya ƙwallo a minti na 11, sai dai China ta rama ƙwallonta ta hannun Zhang Junhao minti 10 baya.
-
Nasarawa Amazons ta lashe Gasar Shugaban Ƙasa ta Tarayya ta Mata ta 2026
- Gasar Cin Kofin Mata na Afirka: Madugu ya gayyaci Ajibade da Oshoala
Duk da cewa tawagogin biyu sun samu dama bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, babu wanda ya iya samun ƙwallon nasara, wasan ya ƙare da kunnen doki.
Wannan sakamakon ya bai wa Najeriya maki na farko a gasar gabannin dawowar ta gida don ci gaba da shirin gasar WAFUB U-17.
