El-Kanemi Warriors FC, ta zama zakarar gasar Shugaban Kasa ta Tarayya ta Maza ta 2026 bayan lallasa Ikorodu City FC da ci 1-0 a wasan karshe.

Wasan ya fara ne da karfe 4:00 na yamma, yayinda alkalin wasa na FIFA Kazim daga Kwamitin alƙalai na Jihar Zamfara ya jagoranci wasan.

Muktari Ismail ne ya zura bugun fenareti a rabin farko, abinda ya baiwa El-kanemi Warriors nasara.

Sai dai ‘yan wasan Ikorodu sun kai hare-hare da dama domin farkewa amma hakarsu bai cimma ruwa ba.

A halin yanzu, El-Kanemi Warriors ta samu tikitin wakiltar Najeriya a Gasar CAF Confederation Cup, tare da Shooting Stars ta Ibadan, wadanda suka kare a matsayi na uku a teburin Gasar Kwararrun Kungiyoyin Kwallon Kafa na Najeriya, wato NPFL.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *