Tsohon kocin Senegal Pape Thiaw

Hukumar ƙwallon ƙafar Senegal, FSF, ta sanar da sallamar kocin tawagar ƙasar, Pape Thiaw, tare da dukkan masu taimaka masa nan take, abin da ya kawo ƙarshen aikin sa tare da tawagar ƙasar, ta Teranga Lions.

Hukumar ta tabbatar da hakan ne cikin sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi, biyo bayan rashin samun sakamako mai kyau da tawagar Senegal ta samu a gasar Cin Kofin Duniya ta 2026.

“Bayan nazari sosai kan ƙoƙarin tawagar na kwanan nan, FSF ta yanke shawarar kawo ƙarshen kwantiragin kocin tawagar, Pape Thiaw, da masu taimaka masa nan take,” inji sanarwar Hukumar.

Sai dai hukumar ta FSF ba ta bayyana sunan wanda zai riƙe matsayin na wucin gadi ko na din-din-din ba tukuna.

Amma majiyoyi dake kusa da hukumar sun ce za a fara neman sabon koci nan take domin shirya Senegal zuwa gasar neman tikitin shiga cin kofin nahiyar Afirka, AFCON, da sauran wasannin ƙasa da ƙasa masu zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *