Dakarun sojin Sector 7 sun kama wasu da ake zargin masu safar makamai ne tare da kuma kwato bindigogi bakwai da aka mallaka ba bisa ka’ida ba a yayin wani aiki na binciken motoci da aka yi a garin Samaru da ke karamar hukumar Zangon Kataf a Jihar kaduna.
Majiyoyin leken asiri sun shaida wa zagazola makama cewa an gudanar da aikin ne da misalin karfe 9:40 na safiyar ranar Litinin, bayan samun sahihin bayani kan yadda ake safarar makamai ba bisa ka’ida ba daga Jos, Jihar Filato, zuwa Jihar Naija.
A cewar majiyar, sojojin sun samu bayanin cewa wasu da ake zargi da safarar makamai suna dauke da makaman ne a cikin motar Mercedes-benz mai launin toka, bayan bin diddigi, sannan suka kama motar a Samaru da ke Zangon Kataf.
- ‘Yan Sandan Abuja sun gurfanar da mutum 3 gaban Kotu kan zargin kisan kai
- Sojoji sun kama mota ɗauke da miyagun ƙwayoyi
Bayan cikakken bincike a cikin motar, an samu bindigogi kirar AK-47 guda uku, kirar gida da kuma bindigogi kanana na inji guda hudu da SMGs da aka boye cikin motar.
A lokacin gudanar da binciken, daya daga cikin wadanda ake zargin ya yi kokarin tserewa, amma sojoji sun harbe shi, inda ya ji rauni kuma nan take aka kai shi cibiyar kiwon lafiya ta Sojoji ta Sector 7 dake Kafanchan domin yin jinya.
An bayyana wannan kame a matsayin wata babbar nasara a kokarin da jami’an tsaro ke yi na katse yaduwar makamai ba bisa ka’ida ba dake kara wa laifuka da rashin tsaro karfi a yankin Arewa ta tsakiya.
Hukumomin tsaro sun ce ana ci gab da gudanar da bincike domin gano da kuma cafke duk wanda ke da hannu cikin harkar safar makaman.
Majiyoyin soji sun ce ana ci gaba da tsare wadanda ake zargin tare da makaman da aka kwato, kuma za a mika su ga hukumomin da suka dace a hedkwata domin ci gaba da bincike da nufin ruguza hanyar safarar makamai da cafke sauran mambobin kungiyar.