Matatar mai ta Dangote ta fara saka farashin dalar Amurka kan man da take sayarwa ga masu buƙata a defo ɗinta.

Bayanin wannan sabbin farashin ya zo ne a wata sanarwa da aka aike wa dillalan mai, wadda kuma ta jaddada cewa sabon tsarin ya soke duk wata odar da aka yi kan farashin naira.

Sauyin salon tsayar da farashin tattacen mai daga naira zuwa dala ya fara aiki ne ranar Litinin 13 ga Yuli, inda farashin mai samfurin PMS yake a dala $0.779 duk lita  sai man dizal wanda ya koma $1.087 duk lita.

Sai kuma man jiragen sama wanda ya tsaya kan dala $0.942 duk lita. Nau’in man LPG ne kawai sauyin bai shafa ba.

Wannan na nuna cewa an kawo ƙarshen shirin Matatar Dangote da gwamnatin Nijeriya na sayar da ɗanyen man ƙasar kan farashin naira ga matatar, domin matatar ta sayar da tataccen mai kan naira a ƙasar.

Tun a Oktoban 2024 ne matatar ta shiga wannan shiri, wanda aka ci gaba da sabuntawa lokaci bayan lokaci saboda yana amfanar ‘yan Nijeriya da kuma tattalin arziƙin ƙasar.

Idan za a tuna dai, a ranar 1 ga watan Oktoban 2024 ne gwamnati ta fara sayar da ɗanyen mai a kan naira ga matatar man Dangote domin inganta samar da man fetur, lamarin ya kai ga taimaka wa ƙasar nan da samun rarar miliyoyi na dala da take narkawa wajen sayo ɗanyen mai daga ƙasashen waje, kuma shirin ya taimaka sosai wajen samun ragi kan farashin fetur.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *