Shugaban Jami’ar Jihar Yobe (YSU), Farfesa Muhammad Bashir Tahir, ya jinjina wa Gwamna Mai Mala Buni bisa amincewa da aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar da Gwamnatin Tarayya ta kulla da Kungiyar Malaman Jami’o’i (FGN/ASUU) ta shekarar 2025, inda ya bayyana cewa matakin zai karfafa ilimi mai zurfi tare da inganta walwalar malaman jami’o’i a jihar.
A cikin wata sanarwa da Ofishin Shugaban Jami’ar ya fitar ranar Litinin, Farfesa Tahir ya bayyana wannan amincewa—da ta haɗa da biyan dukkan tulin basussukan da ake bin gwamnati na alawus-alawus na malaman jami’ar—a matsayin wani gagarumin mataki na tarihi da ke nuna irin jajircewar gwamnan ga fannin ilimi.
Ya bayyana cewa aiwatar da yarjejeniyar zai bunƙasa karsashin aiki na malamai, ya inganta koyarwa da bincike da kirkire-kirkire, sannan zai ƙara rura wutar gudanar da aiki yadda ya kamata a dukkan manyan makarantun jihar.
“Amincewa da aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar FGN/ASUU, tare da biyan dukkan alawus-alawus da ke ƙasa, babban nuni ne na hangen nesa irin na Gwamna Mai Mala Buni da kuma sahihiyar sadaukarwarsa ga bunƙasar ilimi mai zurfi,” in ji Tahir.
- Najeriya ta yi asarar Naira tiriliyan 34 sakamakon rangwamen harajin shigo da kaya – Kwastam
- Sojoji sun kama masu yi wa ‘ yan bindiga safarar makamai daga Jos
- Abubuwan ban-mamaki 5 game da Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani
A cewar shugaban jami’ar, wannan shawara za ta bar tarihi mai kyau na dogon lokaci a Jami’ar Jihar Yobe da ma fannin ilimi na jihar baki ɗaya.
Haka zalika, shugaban jami’ar ya yaba wa irin jarin da gwamnan yake zubawa a fannin ilimi, inda ya buga misali da samar da ababen more rayuwa, shirye-shiryen horar da ma’aikata don ci gabansu da tallafawa binciken kimiyya da tsarin ba da gurbi da tallafin karatu (scholarship), da sauran manufofi da nufin inganta ingancin koyarwa da koyo.
Ya bayyana Gwamna Buni a matsayin gwarzon fannin ilimi da lafiya, yana mai cewa gwamnatin ta samu gagarumar nasara a ɓangarorin biyu ta hanyar zuba jari a fannin ababen more rayuwa, sauye-sauye a hukumance da ɓunkasa ma’aikata, da inganta yadda ake isar da ayyuka.
A cewarsa, Jami’ar Jihar Yobe ta sami ci gaba mai gamsarwa a ƙarkashin gwamnati mai ci ta hanyar gina rukunonin azuzuwa na zamani, inganta kayayyakin koyo, da kuma samar da karin damammaki na horarwa da ci gaban ma’aikata.
Tahir ya ƙara da cewa, aiwatar da yarjejeniyar ta FGN/ASUU zai taimaka wajen riƙe ƙwararrun malamai a jami’ar, rage asarar ƙwararru zuwa ƙasashen waje (brain drain) da ƙarfafa gwiwar kirkire-kirkire, da kuma inganta darajar jami’ar a gasar da ke tsakanin manyan makarantun ƙasar nan.