Majalisar Wakilai ta soke amincewar da ta yi a baya kan kudirin gyaran kukafawa dasarin mulki da ke neman kafa Hukumar ‘Yan Sandan Jihohi a faɗin Najeriya, bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa nasa Kudirin ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
A baya, Majalisar ta amince da na ta kudirin a ranar 11 ga Yuni, 2026, sannan ta kafa kwamitin sulhu mai mambobi 12 domin daidaita bambance-bambancen da ke tsakanin sigar kudirin da Majalisar Wakilai ta amince da shi da kuma wadda Majalisar Dattawa ta amince da shi.
Sai dai bayan isowar kudirin da bangaren zartarwa ya gabatar, Majalisar ta ce sabbin batutuwa da suka shafi tsarin kafawa da gudanarwa da aiwatar da Hukumar ‘Yan Sandan Jihohi sun sa ya zama dole a bi sabuwar hanyar doka domin tabbatar da an samar da tsarin kundin mulki mai cike da inganci, kuma ya dace da buƙatun tsaron ƙasa.
- Zamu riƙa sayar da mai da Dala ga yan kasuwa – Ɗangote
- Amincewar da Buni ya yi wa yarjejeniyar ASUU zai bunkasa ilimi da walwalar ma’aikata — Shugaban Jami’ar Jihar Yobe
- Najeriya ta yi asarar Naira tiriliyan 34 sakamakon rangwamen harajin shigo da kaya – Kwastam
Majalisar ta ɗauki wannan mataki ne bayan amincewa da ƙudurin da Shugaban Kwamitin Dokoki da Harkokin Kasuwanci, Hon. Francis Waive (APC, Delta), ya gabatar, wanda ya nemi a soke kudirin da aka amince da shi a baya tare da rusa kwamitin sulhun da aka kafa.
Hakan ya ba da damar Majalisar ta fara nazarin Kudirin Gyaran Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (Gyara), 2026 (HB. 2797), wanda Shugaba Tinubu ya gabatar.
Majalisar ta bayyana cewa matakin da ta ɗauka ba yana nufin ta janye goyon bayanta ga kafa ‘Yan Sandan Jihohi ba.
A cewarta, manufar ita ce yin aiki tare da bangaren zartarwa domin samar da kundin tsarin mulki da zai tabbatar da kafa Hukumar ‘Yan Sandan Jihohi cikin tsari mai inganci da ya dace da ƙalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta.