A ranar Talata idon duniya zai koma kan wasan kusa da na ƙarshe na Gasar Cin Kofin Duniya tsakanin Sifaniya da Faransa.
Amma me ya sa ake ganin wannan wasa yana da matuƙar muhimmanci?
Da farko, ƙasashen biyu suna cikin manyan ƙasashen da suka mamaye harkar ƙwallon ƙafa a duniya.
Sifaniya ta kai wannan mataki ne bayan ta doke Austria da ci 3-0, sannan ta fitar da Portugal da ci 1-0 kafin ta yi nasara kan Belgium da ci 2-1 a matakin kwata fainal.A ɓangaren Faransa kuwa, ta fara da doke Sweden, sannan ta fitar da Paraguay kafin daga bisani ta doke Morocco da ci 2-0 domin samun gurbin wasan kusa da na karshe.Abin da ya ƙara ɗaukar hankali shi ne tarihin haduwar ƙungiyoyin biyu.
- Gasar Cin Kofin Duniya: Kocin Faransa ya magantu kan raunin Kyalian Mbappe
- Taurarin Faransa sun mayar da martani ga Lamine Yamal
Sifaniya ce ta yi nasara a kan Faransa a wasan kusa da na ƙarshe na Gasar Cin Kofin Euro 2024, sannan ta sake doke ta a UEFA Nations League.
Saboda haka, wannan wasa wata dama ce ga Faransa ta rama wannan kaye da ta sha har karo biyu.
A wajen Sifaniya, ana sa ran matasan taurari irin su Lamine Yamal da Nico Williams za su taka muhimmiyar rawa, yayin da Faransa za ta dogara da ƙwarewar Kylian Mbappé da Ousmane Dembélé wajen neman tikitin zuwa wasan ƙarshe.Masana da dama sun ce babu wata tawaga da za a iya cewa za ta yi nasara a wannan karawar.