Kylian Mbappe ya bayyana cewa shi da sauran abokan wasansa na ƙasar Faransa ba su nuna bajintar da ta dace ba domin kaiwa ga wasan ƙarshe na Gasar Cin Kofin Duniya na shekarar 2026, biyo bayan dukan 2-0 da ƙasar Sipaniya (Spain) ta yi musu a ranar Talata.

Faransa ta shiga wasan a matsayin wadda aka fi tsammanin za ta yi nasara, sai dai dakarun na Didier Deschamps sun tsinci kansu cikin tsaka mai wuya inda Sipaniya ta mamaye wasan ta hanyar amfani da dabarun tazarar gaba da kwarewa ta zahiri.

Ƙwallaye biyu da Mikel Oyarzabal da Pedro Porro suka zura ne suka tabbatar da gurbin Sipaniya a wasan ƙarshe na Kofin Duniya, tun bayan karon ƙarshe da suka lashe gasar a Afirka ta Kudu a shekarar 2010.

‘Yan wasan na Luis de la Fuente sun mamaye wasan gaba ɗaya, inda suka takaita Faransa ga yin harbi biyu kacal da suka nufi raga a duk tsawon wasan. Kafin wannan wasan, Faransa ta riga ta zura ƙwallaye 16, sai dai Sipaniya ta sa gaba ɗaya Mbappe da sauran abokan harinsa sun gaza tabuka komai a ranar Talata.

Ɗan wasan gaba na kungiyar Real Madrid, Kylian Mbappe, ya bayyana bajintar tawagar Faransa a matsayin abin takaici kuma wadda ba ta dace da samun gurbin zuwa wasan ƙarshe ba.

Ya ce “Ba mu nuna irin bajintar da muke buƙata ba, ta fuskar dabarun wasa, kwarewa, ko ma yanayin wasanmu na gaba ɗaya,” in ji Mbappe.

“Yayin da ka gaza yin abin da ya kamata ka yi a wasan kusa da na ƙarshe na Kofin Duniya, ba za ka yi nasara ba.

“Sipaniya ta tsaya kan tsarin wasanta da abin da ta yi imani da shi. Akwai rashin kyakkyawar sadarwa a lokacin da muke matsa musu lamba, kuma ko da mun ƙwaci ƙwallo, fasfofinmu na farko da taɓa ƙwallonmu na farko ba su dace da wasan kusa da na ƙarshe na Kofin Duniya ba,” in ji shi.

Yayin da yake zantawa da manema labarai bayan wasan, kocin Faransa, Didier Deschamps, ya ce ƙungiyarsa ta sha kashi ne a hannun ƙungiyar da ta fi ta ƙwazo.

Mbappe ya ƙara da cewa: “’Yan wasan sun shiga matsananciyar damuwa, amma dole ne mu fito fili mu faɗi gaskiya: ta fuskar ƙwarewa, mun kasance na baya. Kuma laifinmu ne.”

Pedro Porro, wanda ya zura ƙwallo ta biyu ga Sipaniya, ya bayyana cewa wannan nasara babban mafarki ne da ya zama gaskiya a gare shi, kuma ya ƙara da cewa ƙungiyarsa ta yi duk abin da ya dace don fuskantar babbar ƙungiya kamar Faransa.

Ya ce: “Gaskiya babban mafarki ne ya zama gaskiya. Ban taɓa tunanin samun abu makamancin haka ba, ko da a mafarkina mafi ban-mamaki,” in ji Porro.

“Mun yi duk abin da ya dace a kan ƙungiyar da ta nuna gagarumar bajinta a wannan Kofin Duniya,” in ji shi.

Sipaniya za ta san ƙasar da za su fafata da ita a wasan ƙarshe bayan da ƙasar Ingila za ta fuskanci Argentina a birnin Atlanta domin neman gurbin shiga wasan ƙarshe na ranar Lahadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *