Hukumomin Kiwon Lafiya na Falasɗinu sun ce hare-haren jiragen yaƙi na Isra’ila a Gaza sun kashe aƙalla mutum 12 cikin kwanaki biyu da suka gabata.
Cikin waɗanda aka kashe akwai iyalai uku da aka ce an kashe su a tsakiyar Gaza ranar Laraba, da kuma wani yaro da sojojin Isra’ila suka harba a wajen birnin Rafah.
A ranar Talata ma, an kashe wata mace tare da ‘yan sanda shida a wani harin bam da aka kai a ofishin ‘yan sanda da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Jabaliya a Arewacin Gaza.
-
Trump ya yi barazanar kai farmaki kan muhimman ababen more rayuwa na Iran
-
Iran ta gargadi cewa yaƙi na gaba zai kama zuwa yaƙin duniya
-
Ba za mu lamunci hare-hare kan Ƙasashen Larabawa ba – Nabil Fahmy
Sojojin Isra’ila sun ce huɗu daga cikin ‘yan sandan ‘yan Hamas ne amma ba su fitar da wata shaida ko hujja mai ƙarfi ba.
A halin yanzu, ofishin Majalisar Dinƙin Duniya mai kula da kare hakkin bil’adama ya yi Allah-wadai da kai hari kan ‘yan sandan Gaza, inda ya ce an kai musu hari aƙalla sau goma sha biyu wannan shekara har da lokacin da suke gudanar da aikin yau da kullum.
Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce mutum 1,100 aka kashe tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara a watan Oktoba.
Bangaren Isra’ila kuma ta ce sojoji biyar aka kashe tun daga lokacin, bayan ‘yan bindigar Falasdinu suka kai musu hari.
Isra’ila na cewa harin nata na martani ne ga wadancan hare-hare da sauran take hakkin.
