Kungiyar Masu Mallakar Gidajen Sayar da Man Fetur na Kasa (PETROAN) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hanzarta farfado da matatun mai na gwamnati da ke kasar, biyo bayan matakin da Matatar Mai ta Dangote ta dauka na dakatar da sayar da man fetur da kudin naira tare da komawa amfani da dalar Amurka a kasuwancinta.
Shugaban kungiyar PETROAN na kasa, Dr. Billy Gillis-Harry, ya bayyana cewa gudanar da ayyuka a matatun mai na Port Harcourt, Warri, da Kaduna zai zama babbar hanyar daidaita farashin mai a sashen kasuwancin mai na kasa, sannan zai hana kamfani guda daya mamaye kasuwa.
Da yake jawabi a birnin Legas ranar Laraba, Gillis-Harry ya ce ko da yake ƙungiyar tana goyon bayan janye tallafin mai da barin kasuwa ta gudanar da kanta, matakin da matatar Dangote ta ɗauka ya nuna buƙatar samun matatun mai da yawa masu aiki domin samar da gasar kasuwanci, kare hakkin masu amfani da mai, da kuma karfafa tsaron samar da makamashi a Najeriya.
- Hare-haren Isra’ila a Gaza sun kashe aƙalla mutum 12
- Gobara ta hallaka aƙalla mutane 11 a Gidan marayu da ke Aljeriya
- Tinubu ya ƙaddamar da rukunin samar da ruwa na Bwari, Ya yi kardadon faɗaɗa samar da ruwa a FCT
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Matatar Dangote ta koma yin ciniki da dalar Amurka ne sakamakon kusan durkushewar tsarin nan na sayar da danyen mai da naira (crude-for-naira) wanda gwamnatin tarayya ta bullo da shi.
Shugaban ƙungiyar PETROAN ya nuna damuwa kan cewa ‘yan kasuwar mai suna samun kudaden shiga ne da naira, amma yanzu za a bukaci su nemo dalar Amurka domin siyan kayyakin mai. Ya yi gargadin cewa wannan zai kara kudin gudanar da kasuwanci, ya jefa ‘yan kasuwa cikin hadarin sauyin farashin dala, sannan ya kara wa talakawa nauyi.
Saboda haka, ya yi kira ga Babban Jami’in Gudanarwa na Kamfanin NNPCL, Engr. Bayo Ojulari, da ya ba da umarnin fara gudanar da ayyukan wucin gadi a matatun mai na Port Harcourt, Warri, da Kaduna, yayin da ake ci gaba da tattaunawa da wasu abokan hulda na kasar Sin (Chinese partners) guda biyu masu fannin fasaha.
Gillis-Harry ya tunatar da cewa matatun suna aiki kafin a rufe su a watan Mayun 2025, kuma samar da mai na wucin gadi zai taimaka wajen samar da mai a cikin gida, rage hauhawar farashi, da kuma sauƙ aƙawa ‘yan kasa kafin a kammala yarjejeniyar hadin gwiwar.
Ya jaddada cewa tsaron makamashin Najeriya na dogon lokaci ba zai iya dogaro da matatar mai guda daya ba, ko da kuwa tana da girman gaske.