Gwamnatin Amurka ta ce ta sanya dokar hana ‘yan ƙasar Amurka da suka kasance a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo cikin kwanaki 21 da suka gabata daga shiga ƙasar ta hanyar jirgin sama na kasuwanci, saboda ɓarkewar cutar Ebola.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ce ta wallafa wannan sanarwar a shafin intanet ranar Laraba.
A cewar sanarwar, duk wanda ya kasance a DRC cikin kwanaki 21 kafin tashi, ba za a bar shi ya hau jirgin da ke zuwa Amurka ba.
-
Hare-haren Isra’ila a Gaza sun kashe aƙalla mutum 12
-
Gobara ta hallaka aƙalla mutane 11 a Gidan marayu da ke Aljeriya
-
Trump ya yi barazanar kai farmaki kan muhimman ababen more rayuwa na Iran
Ma’aikatar ta kuma shawarci duk ‘yan Amurka da suka kasance a Congo su shirya zama a wajen ƙasar na tsawon kwanaki 21 kafin su koma Amurka.
Wannan sabuwar doka ta zo ne a daidai lokacin da cutar Ebola ke ci gaba da yaɗuwa zuwa wasu daga cikin lardunan Congo da dama.
Ƙididdigar hukuma ta Congo ta ƙarshen ranar Lahadi ta nuna cewa an samu tabbatattun mutum dubu 1,926 da suka kamu da cutar, inda mutum 702 suka rasu.