Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sakkwato ta ce ta samu nasarar kuɓutar da dukkan mutanen da aka sace a hare-hare biyu da ‘yan bindiga suka kai a ƙananan hukumomin Rabah da Binji.
Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, Hayatu Hassan Shaffa, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar hedkwatar rundunar a Sakkwato
Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, Hayatu Hassan Shaffa, ya ce jami’an rundunar tare da haɗin gwiwar sojoji sun yi artabu da ‘yan bindigar, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa cikin daji tare da ceto waɗanda aka yi garkuwa da su ba tare da sun ji rauni ba.
- ‘Yan kasuwa na neman a farfado da matatun mai
- Gobara ta hallaka aƙalla mutane 11 a Gidan marayu da ke Aljeriya
Ya kuma bayyana cewa a wani samame da aka kai a Bodinga da kuma Daraye da ke Wamakko, jami’an tsaro sun kashe wasu ‘yan bindiga huɗu tare da ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 biyu da alburusai masu rai.
A cewarsa, rundunar za ta ci gaba da matsa wa masu aikata laifuffuka domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.