‘Yan sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) sun ce sun fara bincike kan wani lamari da ya faru a ƙaramar hukumar Bwari, inda ake zargin wata mata mai suna Mercy da yanke wani ɓangare na gashin ‘yar maƙwabciyarta da ƙarfi bayan wata takaddama da ta shiga tsakaninsu.
Lamarin, wanda ya faru a unguwar Kogo da ke garin Bwari, ya jawo fargaba a tsakanin mazauna yankin bayan zargin cewa matar ta tsere da gashin yarinyar bayan ta yi barazanar amfani da shi wajen cutar da ita. Mahaifiyar yarinyar ta ce ta kai rahoton lamarin ofishin ‘yan sanda na Bwari.
A cewar mahaifiyar, takaddamar ta samo asali ne daga wata saɓani da ta yi da wadda ake zargin, inda ta ce al’amarin ya ƙazanta har ta kai ga Mercy ta mari ta. Ta ƙara da cewa lokacin da ‘yarta ta yi ƙoƙarin shiga tsakani, wasu mata tare da Mercy suka riƙe ta, sannan Mercy ta fitar da almakashi ta yanke wani ɓangare na gashinta.
-
‘Yan sanda sun kama masu garkuwa da masu bai wa ‘yan bindiga bayanai da masu safarar miyagun ƙwayoyi
-
Tinubu ya ƙaddamar da rukunin samar da ruwa na Bwari, Ya yi kardadon faɗaɗa samar da ruwa a FCT
Mahaifiyar ta ce bayan aikata hakan, Mercy ta tsere ɗauke da gashin yarinyar, kuma duk ƙoƙarin gano ta da kuma ƙwato gashin bai yi nasara ba. Ta kuma yi zargin cewa Mercy ta yi barazanar “koya wa ‘yarta darasi” ta hanyar amfani da gashin da ta ɗauka.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce barazanar ta ƙara tayar da hankalin al’umma. A halin da ake ciki, rahotanni sun ce ‘yan sanda sun kama wasu mata biyu, Nnenna da Helen, bisa zargin ɓoye Mercy a wani gidan karuwai da ke yankin, sai dai daga baya an sake su beli tare da umurtarsu su gabatar da wadda ake nema kafin ranar Litinin.
Jami’in kula da ofishin ‘yan sanda na Bwari (DPO), CSP Babayola Muhammad Musa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa bincike kan zargin na ci gaba domin gano gaskiyar abin da ya faru da kuma kamo wadda ake zargi.