Ƙungiyar Tallafawa Manoma Mata (WOFAN) ta ƙaddamar da wata gadar ƙasa (ta masu tafiya a ƙasa), da rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana (solar), da kuma hanyar mota a al’ummar Danbare da ke Jihar Kano.

Yayin da take jawabi a wajen taron ƙaddamarwar, Shugabar Hukumar Gudanarwar WOFAN, Dr. Salamatu Garba, ta bayyana cewa an tsara waɗannan ayyuka ne bayan dogon tattaunawa da mutanen yankin domin gano ainihin matsalolin da suka fi addabar su.

“Mun nuna cewa ba lallai ba ne al’ummomi su riƙa jiran gwamnati a kowane lokaci don magance kowace matsala. Lokacin da mazauna yankuna, hukumomi, da ƙungiyoyin haɗin gwiwa suka yi aiki tare, za su iya samar da mafita mai amfani da ke inganta rayuwa,” in ji ta.

Ana sauran waɗannan ayyuka za su amfani mazauna Danbare, ɗaliban Makarantar WOFAN (WOFAN Comprehensive School), ɗaliban kusan makarantun gwamnati da na masu zaman kansu guda 10 da ke maƙwabtaka da yankin, ɗaliban Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) da ke zaune a wajen makarantar, da sauran masu amfani da babbar hanyar Gwarzo.

Dr. Salamatu ta ƙara da cewa gadar za ta sauƙaƙa hanyar zuwa kasuwanni, ta ƙarfafa alaƙa tsakanin al’ummar yankin da maƙwabta, sannan ta inganta rayuwar mazauna gaba ɗaya.

Ta bayyana cewa an gina waɗannan abubuwa ne domin magance matsalolin gaggawa na al’umma, wanda hakan zai kawo amintacciyar zirga-zirga ga masu tafiya a ƙasa, ingantacciyar hanya, da kuma dorewar samar da ruwan sha mai tsafta.

Rijiyar mai amfani da hasken rana tana ɗauke da wuraren ɗashen ruwa sama da 12, wanda zai samar da ruwa cikin sauƙi, yayin da sabuwar hanyar kuma za ta bunkasa harkokin tattalin arziki a yankin.

Ta yi kira ga mazauna yankin da su kare tare da kula da waɗannan kayayyaki, tana mai jaddada cewa dorewarsa ta dogara ne ga yadda al’umma suka ɗauke shi a matsayin nasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *