Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi Canada da haddasa hadarin hayaƙi da ya fito daga gobarar daji da ya lulluɓe kaso mai yawa na Amurka.

A wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya yi hasashen cewa Ottawa bata tafiyar da dazukanta yadda ya kamata, inda yake zargin Canada da ƙyale iska mai datti da haɗari ta afka wa Amurka.

Shugaban na Amurka  ya yi barazanar ƙara kuɗin wannan gurɓata iskar cikin harajin da zai ƙaƙaba wa kayayyakin da Canada ke fitartwa a Amurka.

Trump ya nuna cewa zai iya magana daga baya da Firayimministan Canada domin gano matakan da ake shiryawa don sauƙaƙa yanayin

Shugaban na Amurka ya zargi Canada da ƙin ɗabbaka matakai na kula da daji da kuma nome ciyawa, yana mai bayyana shi a matsayin “rashin kula na gangan.” Ya ce waɗannan lamurran na faruwa a ko wace shekarar kuma Amurka na rasa “biliyoyin daloli” sakamakonsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *