Magajin Garin birnin New York, Zohran Mamdani, ya bayyana cewa yana tattaunawa da masu ba shi shawara kan harkokin shari’a domin tantance ko yana da ikon ɗaukar matakin kama Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, idan ya halarci babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya da za a gudanar a watan Satumba.

Mamdani ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar The New York Times ta wallafa a ranar Asabar, 18 ga Yuli, 2026.

Magajin garin, ya taɓa kiran Isra’ila da “ƙasar wariyar launin fata (apartheid),” ya ce wannan ra’ayi ba nasa kaɗai ba ne, yana mai cewa mutane da dama suna kallon hakan ne bisa abin da ya ce manufofi da ayyukan Netanyahu suka haifar tsawon shekaru.

Sai dai Mamdani ya amince cewa har yanzu bai da tabbacin ko yana da ikon umartar Rundunar ‘Yan Sandan New York (NYPD) ta kama wani shugaban ƙasa ko gwamnati na ƙasashen waje.

Ya ce a halin yanzu yana tattaunawa da lauyoyin birnin domin sanin iyakar ikon da doka ta ba shi.

A baya, Mamdani ya sha alwashin cewa idan doka ta ba shi dama, zai umarci Rundunar ‘Yan Sandan New York ta aiwatar da sammacin kama shugabannin da Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ke nema ruwa a jallo, ciki har da Firaminista Benjamin Netanyahu da Shugaban Rasha, Vladimir Putin.

Ana sa ran babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UN General Assembly), wanda ke haɗa shugabannin ƙasashe daga sassa daban-daban na duniya, zai gudana a hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke birnin New York a watan Satumba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *