Tsohon Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero Kano (BUK), Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya ce ana iya kawo karshen matsalar yaran da basa zuwa makaranta a Arewacin Najeriya idan gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki suka haɗa kai tare da aiwatar da manufofin da suka dace.
Farfesa Abbas ya bayyana hakan ne yayin gabatar da jawabi a wani taron tattaunawa da Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya ta shirya kan matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin Arewa.
A jawabin nasa mai taken “ Yaran da Ba Sa Zuwa Makaranta a Arewacin Najeriya: Fahimtar Asalin Matsalar, Sake Nazarin Kalubalen da Kuma Tsara Manufofin da Za Su Samar da Sauyi Mai Ɗorewa,” ya ce magance matsalar na buƙatar jajircewar shugabanni da ingantattun manufofi da isasshen tallafin kuɗi da kuma cikakken haɗin kan al’umma.
- Shatima zai halarci taron ECOWAS na 69
- Katsewar Wutar Lantarki ta shafi jihohi shida a Arewacin Najeriya – TCN
- Abuja na samun ci gaba ƙarƙashin Wike shekaru 50 bayan kafuwarta – Tinubu
Ya bayyana cewa alƙaluma kaɗai ba su isa wajen fahimtar girman matsalar ba, domin akwai dalilai masu yawa na zamantakewa da tattalin arziki da al’adu da kuma tsarin gwamnati da ke hana yara samun ilimi.
A cewarsa, duk yaran da ba sa zuwa makaranta ba rukuni guda ba ne, saboda haka ba za a iya magance matsalarsu da tsari guda ɗaya ba.
Ya ce Arewacin Najeriya na da dogon tarihi a fannin ilimi, musamman ilimin addinin Musulunci, don haka bai dace a ɗauki yankin a matsayin wanda ba ya son ilimi ba.
Farfesa Abbas ya yi nuni da cewa bayanan UNICEF sun nuna yara kusan miliyan 18 ne ba sa zuwa makaranta a Najeriya, inda mafi yawan su ke yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.