Wilfred Ndidi

Kungiyar Besiktas ta kasar Turkiyya da ke doka gasar Super Lig ta ki amincewa da tayin Yuro miliyan 7 da kungiyar Al Drimah ta yi don siyan dan wasan tsakiya na Najeriya, Wilfred Ndidi.

An gano cewa Besiktas ta sanya farashin Yuro miliyan 10 ga tauraron Super Eagles din kuma ba ta shirya karbar tayin farko da kungiyar Al Drimah ta gabatar mata ba.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa Besiktas na iya saukaka farashin zuwa Yuro miliyan 8 idan tattaunawa ta ci gaba.

Ndidi na daya daga cikin manyan ‘yan wasan da Al Drimah ke so ta saya, amma duk wata yarjejeniya za ta dogara ne kan ko kungiyar za ta kara tayin don kai wa farashin da Besiktas ke so.

Dan wasan mai shekaru 29 yana ci gaba da janyo hankalin kungiyoyi saboda kwarewarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *