Wani abin taba zuciya ya faru a kauyen Dadri Tirgali na karamar Hukumar Ganye ta Jihar Adamawa, a inda tsawa ta fadowa wasu yara su takwas.
An ruwaito cewa nan take shida cikin su suka riga mu gidan gaskiya, yayin da saaura biyu suka jikkata.
Kamar yadda wani wanda abin ya faru a idanunsa ya shaida, haɗarin ya faru ne ranar Lhadi, lokacin da ake ruwan sama kamar da bakin kwarya.
- Spaniya ta lashe Kofin Duniya na shekarar 2026
- Besiktas ta yi fatali da tayin Yuro miliyan 7 kan Ndidi
- Ba ta’addaci ne babbar barazanar Najeriya ba – Kuku
An garzaya da sauran yara biyun da suka tsira zuwa asibiti mafi kusa don samun kulawar lafiya.
Wannan lamarin da ya shammaci al’umar yankin, ya jefa su cikin alhini inda ya bar su cikin jimami da firgici.
Izuwa lokacin tattara wannan labari, hukumomin da bin ya shafa ba su fitar da wani bayani a hukumance ba, sai dai ana ci gaba da ƙoƙarin lalubo ƙarin bayani kan haɗarin.