Kyalian Mbappe, dan wasan gaba na Faransa da Real Madrid

Kylian Mbappe ya lashe Takalmin Zinare na Gasar Cin Kofin Duniya na 2026 da ƙwallaye 10, inda ya zarce Lionel Messi da ƙwallaye biyu. Messi ya ƙare gasar ne da ƙwallaye 8.

Mbappe ya kuma zama ɗan wasa na farko da ya lashe Takalmin Zinare na Kofin Duniya sau 2 a jere. Da farko ya lashe shekaru huɗu baya a Qatar 2022.

Har ila yau, Mbappe shi ne ɗan wasan da ya fi kowa zura ƙwallaye a tarihin Gasar Cin Kofin Duniya da ƙwallaye 22.

Kyalian Mbappe, Dan wasan gaba na Faransa da Real Madrid.

Mbappe ya zama ɗan wasa na 4 kawai a tarihin Kofin Duniya da ya ci ƙwallaye 10 a gasa ɗaya, bayan Fontaine, Gerd Muller na Jamus a 1970 da Sandor Kocsis na Hungary a 1954.

Kafin fara gasar ta 2026, Miroslav Klose ne kan gaba a jerin masu mafi yawan ƙwallaye a tarihin Kofin Duniya da ƙwallaye 16, amma Messi da Mbappe sun zarce tsohon ɗan wasan Jamus din.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *